Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yau Asabar, 10 ga wata Ranar Malala


Pakistan / Malala
Pakistan / Malala
Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yau 10 ga watan Nuwamba a matsayin Ranar Malala, don karrama ‘yar makarantar Pakistan dinnan ‘yar shekaru 15 da haihuwa, mai suna Malala Yousafzai, wadda wani dan kungiyar Taliban ya harbe ta a ka wata guda da ya shige. ‘Yan bindigar sun auna ta ne saboda jaddada ‘yancin mata na zuwa makaranta da ta ke yi da kuma sukar akidar ‘yan bindigar da ta ke yi.

To amman har ilayau, kafar yada labaran Faransa ta ruwaito cewa a daidai lokacin da duniya ke bukin Ranar Malala yau Asabar, ana zama dardar a Mingora, garinsu Malalar, har an dakatar da shirin ‘yan ajinsu Malalar yin shagulgula a bainar jama’a.

Malala dai na wani asibiti a Burtaniya, inda ta ke murmurewa daga raunukan da ta ji kuma likitoci sun ce da alamar za ta warke kwata-kwata.

Tsohon Firayim Minsitan Burtaniya Gordon Brown na Pakistan a yau dinnan Asabar don gabatar da wata takarda mai dauke da sanya hannun mutane sama da miliyan daya ga Shugaba Asif Zardari, ta bukatar kasar Pakistan ta baiwa dukkannin yara a kasar damar samun ilimi.
XS
SM
MD
LG