Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Bakwai Sun Rasa Rayukansu a Wani Hari a Nairobi


Hari da aka kai kan motar safa a Kenya
Hari da aka kai kan motar safa a Kenya
Wata fashewa da ta auku a Nairobi babban birnin kasar Kenya ta kashe mutane a kalla bakwai.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross tace a kalla wadansu mutane 29 sun ji raunuka.

Fashewar da ta auku jiya Lahadi ta faru ne a cikin wata motar safa a wata unguwa da ‘yan kasar Somaliya suka mamaye.

Rahotannin farko sun ce an jefa nakiya ne kan motar, abinda ya haddasa tarwatsewar. Sai dai ‘yan sanda basu tabbatar da haka ba.

Kenya tayi fama da hare-hare da ake asarar rayuka, da ake dora alhakin kan kungiyar mayakan Somaliya da magoya bayanta, dake maida martani sabili da dakarun da Kenya ta tura kasar Somaliya bara
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG