Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Misrawa Sun Yi Gagarumar Zanga-Zanga Talata A Fadin Kasar


Dakarun tsaron Misra sun kama wani dan zanga-zanga lokacin arangama a kusa da dandalin Tahrir a al-Qahira, Talata 27 Nuwamba 2012.
Dakarun tsaron Misra sun kama wani dan zanga-zanga lokacin arangama a kusa da dandalin Tahrir a al-Qahira, Talata 27 Nuwamba 2012.

Misrawa sun yi gangami a wani yanayi na fusata da tashin hankalin da yayi kama da tayar da kayar baya da aka yi ma tsohon shugaba Hosni Mubarak

'Yan adawar kasar Misra sun yi gangami a fadin kasar talatar nan, a zanga-zangar tayar da kayar baya dake kara yin karfi a kan yunkurin zababben shugaban dimokuradiyya, Mohammed Morsi, na bai ma kansa ikon da ba mai iya kalubalantarsa.

'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a kan 'yan zanga-zanga dake jifa da duwatsu a kusa da dandalin Tahrir, a wasu al'amuran nuna fusata da tashin hankalin da suka yi kama da wadanda suka kai ga hambarar da tsohon shugaba Hosni Mubarak daga kan mulki a 2011.

Haka kuma, magoya baya da masu yin adawa da shugaba Morsi sun ba hammata iska a arewa da birnin al-Qahira, a ranar da aka yi zanga-zanga mafi muni tun ranar Jumma'ar da ta shige, lokacin da shugaba Morsi ya ayyana kafa wata dokar shugaban kasa da nufin karfafawa da kuma jaddada ikonsa kan shimfida sabuwar akidar siyasa a kasar.

Wannan dokar shugaban kasa zata kare majalisar zana sabon daftarin tsarin mulki wadda 'yan ra'ayin Islama suka mamaye da kuma babbar majalisar dokokin kasar, watau Majalisar Shura, koda kotun kolin kasar zata nemi rushe su.

Kungiyoyin adawa sun bukaci da shugaba Morsi ya soke wannan doka da ya bayar. Sun zarge shi da kokarin ba kansa ikon kama-karya kamar na mutumin da ya gada a kan mulkin.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG