Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Congo Sun Bayyana Cewa Su Na Ficewa Daga Garin Masisi; Sun Kuma Yi Alkawarin Barin Garin Goma.


 Burgediya-Janar Sultani Makenga
Burgediya-Janar Sultani Makenga
Babban kwamandan mayakan kungiyar ‘yan tawayen Congo mai suna M23 ya ce dakarunsa sun fara ficewa daga garin Masisi kuma sun a shirin ficewa daga garin Goma da su ka kama tun farko.

Sultani Makenga ya fadi yau Laraba cewa ‘yan tawayen na barin Masisi, wanda wani karamin gari ne mai nesan kimanin kilomita 50 daga arewa maso yammacin Goma, bayan wata yarjajjeniyar da kasar Uganda ta taimaka aka cimma.

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar, Jean-Marie Runga, ya gaya wa Muryar Amurka jiya Talata cewa zuwa ranar Jumma’a dakarun M23 za su bar Goma, wanda hakan alama ce ta fa’idar da ke tafe. To amman y ace janyewar ba ta nufin cewa kungiyar ta yi watsi da bukatunta cewa ‘yan kasashen waje da dakarun Congo su bar yankin.

‘Yan tawayen sun kama Goma a makon jiya kuma sun kame garin Sake.

Da yammacin ranar Talata, shugaban dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Herve Ladsous ya gaya wa manema labarai cewa akwai alamun da ke nuna cewa lallai kam ‘yan tawayen M23 sun fara janyewa daga garin Goma. Ladsous ya ce Hukumar tabbar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta tantance janyewar a yau dinnan Laraba.
XS
SM
MD
LG