Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin ‘Yan Tawayen Musulmi Na Kasar Mali Sun Sallama Ta’addanci


Mayakan Ansar Dine na kasar Mali
Mayakan Ansar Dine na kasar Mali
Kungiyoyin ‘yan tawayen Musulmi da suka kwace yankin arewacin kasar Mali sun yarda zasu yi watsi da ta’addanci da kuma amfani da karfi ko tayar da hankali domin suyi kokarin cimma hadin kai a wannan kasa mai fama da fitina a Afirka ta Yamma.

An cimma wannan yarjejeniya a bayan tattaunawar da aka yini ana yi jiya talata a tsakanin su da gwamnatin Mali a kasar Burkina Faso, makwabciyar Mali.

Kungiyar Tarayyar Afirka da wasu jami’an kasashen Afirka ta Yamma sun nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta bayar da iznin tsoma hannun sojojin kasashen waje a Mali, saboda fargabar cewa ‘yan tsagera zasu yi kokarin kafa kasa mai bin tafarkin Islama zalla. Masu kishin addinin sun riga sun kama birnin Timbuktu mai dimbin tarihi, har ma sun haramta wasu abubuwan da ake alakantawa da al’adun Turai, kamar wakoki.

An dauki kasar Mali a zaman daya daga cikin kasashen dake da kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma kafin sojoji su hambarar da gwamnatin kasar a watan Maris. Wannan ya haddasa wani lokaci na rashin mai iko a kasar, har kungiyar kishin Islama ta Ansar Dine da ‘yan tawayen kabilar Abzinawa da suka taya tsohon shugaba Muammar Gaddafi na Libya fada, suka samu zarafin kutsawa suka mamaye arewacin kasar.

Jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana damuwa kan lamarin da ake ciki a arewacin Mali, amma sun yi gargadi game da daukar matakan soja a wannan lokaci.
XS
SM
MD
LG