Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chadi Ta Tura Sojojinta Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya


Sojojin Chadi
Sojojin Chadi
Kasar Chadi ta tura sojojinta zuwa cikin makwabciyarta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin taimakawa wajen yakar ‘yan tawayen dake barazanar hambare shugaba Francois Bozize.

Jami’an gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun fada jiya talata cewa sojojin kasar Chadi sun shiga kasar a bisa rokon shugaba Bozize.

Shugaba Idris Deby Itno na kasar Chadi, babban aboki ne na shugaba Bozize, wanda ya taimakawa a lokacin ad manyan hafsoshin soja suka kwace mulkin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a 2003.

Wata gamayyar kungiyoyin ‘yan tawaye dabam-dabam da ta kwace garuruwa da dama cikin ‘yan kwanakin nan a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta yi barazanar zata hambarar da shugaba Bozize idan har bai aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ta 2007 ba.
A cikin sanarwar da ta bayar ranar litinin, kungiyar ta bukaci gwamnati da ta biya sojojin ‘yan tawaye wasu kudade kamar yadda aka yi alkawarin za a biya su a bayan da suka mika makamansu, a kuma saki fursunonin siyasa.

Sojojin Chadi, wadanda suka samu nasarar murkushe tawaye sau da dama a yankin gabashin kasarsu, sun taba shiga kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a watan Nuwambar 2010 domin fatattakar ‘yan tawayen wata kungiya mai suna CPJP daga garin Birao da suka kwace a arewa maso gabashin kasar.

Kusan tun daga ranar da ya hau kan mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai arzikin albarkatun kasa, shugaba Bozize yana fama da ‘yan tawaye a kasar.
XS
SM
MD
LG