Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye Sun Sake Kwace Wani Garin


Shugaba Francois Bozize na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Shugaba Francois Bozize na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

'Yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kwace garin Bambari, kilomita 400 daga Bangui, a bayan fadan awa biyu da sojojin gwamnati lahadi.

'Yan tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun sake kwace wani garin, a bayan da suka gwabza da sojojin gwamnati.

Gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen da ake kira Seleka ta kwace garin Bambari jiya lahadi. Shaidu suka ce sojojin gwamnati sun arce daga garin a bayan da aka shafe awa biyu ana musanyar wuta da bindigogi.

Garin Bambari, mai mutane kimanin dubu 40, yana yankin tsakiyar kudancin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tafiyar kilomita 400 cikin mota daga Bangui, babban birnin kasar.

A yanzu haka dai, 'yan tawayen sun kwace garuruwa akalla 8 tun lokacin da suka kaddamar da farmaki a cikin wannan wata.

Gamayyar 'yan tawayen ta Seleka ta yi barazanar hambarar da gwamnatin shugaba Francois Bozize, wanda ta zarga da laifin kasa aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla a shekarar 2007.

A makon jiya, kungiyar ta gabatar da bukatu ciki har da neman gwamnati ta saki fursunonin siyasa, ta kuma biya sojojin 'yan tawaye kudaden da ta yi alkawarin zata ba su bayan da suka mika makamansu.

'Yan tawayen su na ci gaba da kame sassan kasar duk da tayin da kasar Chadi ta gabatar na shirya taron neman sulhu da kuma kiran da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi na a kawo karshen wannan fada, kuma 'yan tawayen su janye daga cikin garuruwan da suka kama.

Kasar Chadi, babbar kawar Mr. Bozize, ta tura sojojinta cikin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin su taimakawa gwamnatinsa.
XS
SM
MD
LG