Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gudan Jini Ya Sa Hillary Clinton Kwanciyar Asibiti


Buddhists pray during a ceremony to commemorate the birth of Buddha, at the Chiang Kai-shek Memorial Hall in Taipei, Taiwan.
Buddhists pray during a ceremony to commemorate the birth of Buddha, at the Chiang Kai-shek Memorial Hall in Taipei, Taiwan.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton na kwance a babban asibiti a birnin New York likitoci na duba ta

An kwantar da sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton a babban asibiti sanadiyar wani gudan jinin da ya toshe ma ta jijiyar jini bayan dogon suman da ta yi a kwanakin baya.

A cikin wata sanarwar da ma’aikatar harakokin wajen ta bayar, ta ce ranar lahadi likitocin Clinton su ka gano gudan jinin a wani gwajin bitar da aka yi ma ta. Su ka ce gudan jinin na da alaka da suman da ta yi bayan faduwar da ta yi a can kwanakin baya.

Ana yiwa Clinton maganin gudan jinin a babban asibitin Presbyterian na Birnin New York. Ana kyautata cewa za ta ci gaba da zama a asibitin har nan da wasu kwanaki biyu domin a tabbatar da ta samu lafiya.

Sanarwar ta ce likitocin Clinton za su ci gaba da duba ta su tantance ko da bukatar kara daukan wani mataki.

Clinton ta ji jiki a ‘yan kwanakin nan, inda ta yi fama da ciwon cikin da ya tilasta ma ta soke yin wasu tarurruka a bainar jama’a da kuma yin wasu tafiye-tafiye. Ranar 21 ga watan disamba ruwan jikin ta ya kare, jiri ya kama ta, ta fadi ta yi dogon suma.
Kafin a kwantar da ita a asibiti ranar lahadi, Clinton ta na gida ta na kara murmurewa.
XS
SM
MD
LG