Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mr. Nelson Mandela Na Kara Samun Lafiya


Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela

Mr.Mandela ya warke kuma ya na ci gaba da kara samun lafiya

Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta ce tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ya warke daga cutar huhun da ta kwantar da shi a kwanakin baya da kuma aikin tiyatar cire mi shi curin duwatsun matsarmama.

A cikin wata sanarwar da ofishin shugaba Jacob Zuma ta gabatar, an ce Mr.Mandela ya murmure sosai kuma ya na ci gaba da samun lafiya.

Mr.Mandela ya ci gaba da karbar magani a gidan shi na Johannesburg. Mr.Mandela gwarzon yaki da akidar bambanci da wariyar launin fata, ya yi makonni uku a kwance a asibiti a cikin watan disamba kafin a sallame shi a ranar ishirin da shida ga watan na disamba.

Nelson Mandela ne bakar fatar Afirka ta Kudu da ya fara shugabancin kasar a shekarar alif dari tara da casa’in da hudu, bayan fitowar shi daga gidan kaso. A shekarar alif dari tara da casa’in da uku aka ba shi kyautar yabo ta Nobel saboda rawar da ya taka wajen kawo karshen tsarin bambanci da wariyar launin fata.
XS
SM
MD
LG