Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Sake Yi Wa Hambararren Shugaba Hosni Mubarak Shari'a


Tsohon shugaban Misra Hosni Mubarak a kotu. Jan. 9, 2012.
Tsohon shugaban Misra Hosni Mubarak a kotu. Jan. 9, 2012.
Wata Kotun kasar Misra ta bada Umarnin a sake yin shari’ar da aka yiwa hambararen shugaba Hosni Mubarak na Misra wanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai.

Kotun daukaka karar ta Misra a yau lahadi ta yanke hukuncin sake yiwa Mubarak mai shekaru 84 da haihuwa kuma tsohon shugaban Misra wata dama domin sake sauraren shari’ar. An zargi Hosnui Mubarak ne da laifin hannu wajen shirya aiwatar da kisan da aka yiwa daruruwan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatinsa, zanga-zangar da ta kawo karsahen salon mulkinsa a Misra a shekarar 2011.

Kazalika, kotun daukaka karar ta yanke hukuncin cewa tsohon Ministan cikin gida a Gwamnatin Mubarak, Habib el-Adly da shima aka yankewa hukuncin daurin rai da rai, shima a sake sauraren shari’arsa, haka suma ‘ya’yan Mubarak biyu, Gamal da Alaa. Amma duk zasu ci gaba da zama a kurkuku saboda akwai wasu zargin da ake masu na dabam a kotunan Misra.
XS
SM
MD
LG