Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Hedkwatar 'Yan Sandan Leken Asiri A Afghanistan

'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.
'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.

Jami’an Afghanistan sun ce ma’aikatan tsaro biyu sun rasa rayukansu sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai wa hedkwatar ‘yan sandan leken asiri ta kasar a birnin Kabul.

Jami’an Afghanistan sun ce ma’aikatan tsaro biyu sun rasa rayukansu sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai wa hedkwatar ‘yan sandan leken asiri ta kasar a birnin Kabul.

‘Yan sandan Afghanistan sun fada cewa wata mota cike da bama-bamai ta tarwatse a dai-dai kofar shiga hedkwatar hukumar tsaro ko kuma “National Directotare of Security” da rana yau Laraba.

Tarwatsewar ta haddasa mugun hayakin da ya turnuke sararin samaniya. Har wala yau an kashe wasu mahara biyar dauke da nakiyoyi yayin da suke fitowa daga mota ta biyu suna kokarin kutsawa cikin hedkwatar.

‘Yan sanda sun ce mota ta biyun ita ma cike take da nakiyoyi amma sun samu sun warwaresu.

Ita dai hedkwatar ‘yan sandan leken asirin kasar tana kusa da wasu gine-ginen gwamnati ne a birnin na Kabul wadanda suka hada da ma’aikatar tsaron cikin gida.

Jami’ai sun ce kusan mutane 30 ne suka samu raunuka a harin wanda ya tarwatsa gilashi da karafa ya baza su kusa da wasu shaguna.Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin a sakon da ta aika ta wayar tafi da gidanka.
XS
SM
MD
LG