Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazuna Wani Gari Da Mayakan Sa Kai Suka Kama Sun Fara Gudu A Mali


Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.
Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.
A Mali mazauna wani gari da mayakan sakai suka kama a farkon makon nan sun fara gudu, yayinda wadansu kuma suka bada labarin ana gwabza fada tsakanin mayakan sakai da sojojin Faransa a wajajen gefen yankin.

Wani dan jarida a yankin ya gaywa wakiliyar Muriyar Amurka Anne Look cewa ya ga mutane masun yawa suna barin Diabaly a yau Alhamis, sun doshi kudanci daga arewacin kasar da ahalin yanzu yake hanun ‘yan tawaye. Ya ce woyoyin tarho a garin sun daina aiki, kuma zauna garin sun bada labarin mayakan sakai sun girke a sassan daban daban na garin.

Ahalinda ake ciki kuma, ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, yace dakarun kasar 1,400 sun isa Mali. Kasar ta ayyana tura dakaru 2, 500 wadanda za su ci gaba da zama kasar har sai kome ya daidaita.

Manyan hafsoshin kasashe dake yammacin Afirka sun ce sojoji daga Najeriya, Nijar, Cadi, da Burkina Faso, da kuma Togo su 2,000 nan bada jumawa ba zasu fara isa Mali daga yau Alhamis, a matsayin wani rukuni da sojoji da Majalisar dinkin duniya ta bada umarnin a tura su domin shawo Kan rikicin kasar.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG