Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Mali Sun Kwato Garin Konna Daga 'Yan Tawaye


Sojojin Mali sun ce dukkan garin Konna ya koma hannunsu bayan da suka yi barna mai yawa ma 'yan tawaye masu kishin Islama

Jami’ai a kasar Mali sun ce sojojin gwamnati dake samun tallafin sojojin Faransa sun kwato gari na biyu da ‘yan kishin Islama suka kwace kwanakin baya.

Jami’ai na yanki sun ce an fatattaki tsagera daga garin Diabaly, mai tazarar kilomita kimanin 400 a arewa maso gabas da Bamako, babban birnin kasar. A ranar alhamis, an bayar da rahoton kazamin fada a tsakanin sojojin Faransa da tsageran a Diabaly, garin da wadannan masu tawaye suka kama a ranar litinin.

Har yanzu ba a samu tabbacin labarin kwace garin na Diabaly daga bakin sojojin gwamnatin Mali ko na kasar Faransa ba.

Tun kafin nan, rundunar sojojin Mali da jami’an Faransa sun ce dakarun gwamnatin Mali sun kwato garin Konna, wanda ke gabas da garin Diabaly.

Rundunar sojojin ta ce ta kwato garin Konna baki dayansa, a bayan da ta yi barna mai yawan gaske ma ‘yan tawaye masu kishin Islama a can. Kwace wannan gari da tsageran suka yi a makon jiya, shi ya janyo Faransa ta shiga cikin wannan fada a kasar da ta yi wa mulkin mallaka.

Da alamun farmakin mako guda da Faransa da kuma sojojin kasashen yankin Afirka ta Yamma suka kaddamar ya ja burki ma ‘yan tawaye masu alaka da kungiyar al-Qa’ida a yunkurinsu na nausawa kudu a cikin kasar Mali, daga yankin arewaci da har yanzu ke hannunsu.

Wakilin Muryar Amurka, Idrissa Fall, ya aiko da rahoto daga Bamako, babban birnin Mali cewa ‘yan kasar Mali sun fito kwansu da kwarkwatarsu su na lalae marhabin da zuwa sojojin Faransa. Yace yara da manya, har ma da shugabannin siyasar da suke ta fada da juna tun juyin mulkin da sojoji suka yi bara, duk sun fito da murya guda su na bayyana godiyarsu ga kasar Faransa.

Jami’an Faransa sun ce a yanzu haka akwai sojojinsu dubu daya da dari takwas a Mali, kuma nan da ‘yan kwanakin dake tafe yawansu zai karu zuwa 2500. Faransa ta ce zasu zauna a kasar har sai an samu kwanciyar hankali.

Manyan hafsoshin soja na Afirka ta Yamma sun ce mayaka dubu 2 daga Najeriya da Nijar da Chadi da Burkina Faso da Togo sun fara isa kasar Mali a wani bangare na rundunar da MDD ta amince a tura kasar.

A halin da ake ciki, shugabannin kasashen ECOWAS ko CDEAO, su na shirin yin taron koli yau asabar a Abidjan, babban birnin Cote D’Ivoire, domin tattauna karin matakan da za a iya dauka na warware rikicin kasar ta Mali. Kafin taron dai, shugaban majalisar zartaswar ECOWAS, Desire Kadre Ouedraogo, yace halin da ake ciki a Mali yana bukatar daukar matakin nan take.

A nan Washington, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, tace Amurka tana bayar da tallafi ga sojojin kasashen waje dake Mali. Ta ce sun tura sojoji masu horaswa guda 100 zuwa Nijar da Najeriya da Burkina Faso da Senegal da Togo da kuma Ghana domin tattauna irin bukatun horaswa da kayan aikin da kasashen suke bukata.
XS
SM
MD
LG