Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Bukin Tunawa Da Jagoran Hankoron Kare Hakkokin Bil Adama Marthin Luther King Jr.


Hoton Marthin Luther King Jr. kennan.
Hoton Marthin Luther King Jr. kennan.
A yau ne Amurkawa ke tunawa da jagoran ayyukan kare hakkokin bil adama Marthin Luther King Jr., ta daukar hutun aiki baki daya domin tunawa da ranar haihuwarsa.

King wanda ya taba yin shugabancin ma’ajamiar Baptist ya yaki wariyar launin fata a shekarun 1950 da 60, mafi yawanci a kudancin Amurka, wajenda bakaken fata suka fuskanci wariyar launin fata a cikin al-umma, da kuma hare-hare basu ji ba, basu gani ba.

An kashe King wanda yayi da’awar zanga-zangar lumana, a wani harin bazata a shekara ta 1968 a lokacin da yake da shekaru 39. Yanzu akwai waje ajje tarihi da akayi masa a nan Washington.

King yayi suna ne bayan da yayi nasarar jagorantar zanga-zanga dangane da wariyar launin fata da akeyi wa bakake akan motocin bus a garin Montgomery, dake jihar Alabama. A tsarin wannan lokaci, dole ne bakake su zauna a bayan bus din, kuma idan bus din a cike take, to dole ne su baiwa fararen fata wajen zamansu.

A shekara ta 1964 ne aka kafa dokar hana wariyar launin fata, a dai-dai shekarar da King din yaci lambar yabo ta Nobel.
XS
SM
MD
LG