Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanyi Ya Halaka 'Yan Gudun Hijira Su 17


Wani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar Sobha
Wani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar Sobha
Kungiyar kare ‘yancin Bil Adama ta kasa da kasa”Amnesty” ta bada rahoton cewar mutane goma sha bakwai ne suka halaka a dalilin bala’in sanyin da ake dankarawa a sansanin ‘yan gudun hijirar Afghanistan.

Don haka kungiyar ke gargadin gaggauta daukan matakan hana sake afkuwar yin watsin da aka yi da sansanonin a shekarar da ta gabata da hakan ya janyo rasa rayukan ‘yan gudun hijira dari saboda rashin kulawa.

Jamai’ar dake magana da yawun kungiyar ta “Amnesty” tace lallai kam da an dauki matakan da suka dace da kuwa an rage yawan asarar rayukan da ake yi ta ‘yan gudun hijira a sansaninsu saboda tsananin sanyi.

Idan za’a tuna a ziyarar aikin da ya kai Daular Kasashen Larabwa, ministan harkokin wajen Pakistan Jalil Abbas Jilani anji yana cewa za’a sako sauran fursunonin da ake tsare dasu nan bada jimawa ba. Sai dai bai yi bayanin dalla-dallar lokacin da za’a sako fursunonin ba.
XS
SM
MD
LG