Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Gao Na Murnar Rabuwa Da 'Yan Tawaye


Sojojin Faransa a tsaye a wata mararraba a kimanin kilomita dari shida da ishirin arewa da Bamako babban birnin kasar Mali
Sojojin Faransa a tsaye a wata mararraba a kimanin kilomita dari shida da ishirin arewa da Bamako babban birnin kasar Mali

Mazauna garin Gao a arewacin kasar Mali na ta shagalin murnar kubuta daga hannun masu tsattsauran ra'ayin Islama

A jiya lahadi mazauna birnin Gao da ke arewacin kasar Mali sun sa kade-kade a kan tituna, sun yi rawa, sun busa taba sigari kuma sun saka tufafi irin na turawa a lokacin da su ke nuna murnar kubuta daga hannun masu tsattsauran ra’ayin Islama.

Ranar asabar sojojin Faransa da na kasar Mali su ka sake kwace garin daga hannun masu tsattsauran ra’ayin Islamar da su ka tsere ba tare da nuna wata turjiya ba. Al’ummar Gao na jin dadin rabuwa da shari’ar Islama a karon farko cikin watanni da dama.

Wakiliyar Muryar Amurka a yammacin Afirka, Anne Look wadda ke Bamako babban birnin kasar Mali, ta tattauna da mazauna garin Gao ta wayar talho, sun shaida ma ta cewa masu tsattsauran ra’ayin Islamar sun buya a wasu kauyukan da ke bayan garin Gao, a kimanin tazarar kilomita goma zuwa goma sha biyar.

Wasu sun ce mutanen Gao na ta farautar duk wani mahalukin da ya taba taimakawa masu tsattsauran ra’ayin da suka mamaye mu su gari, kuma su na jin cewa za a yi mu su hukunci mai radadi. Haka kuma sojojin Faransa da na Mali sun kusa rutsa ‘yan tawayen a birnin Timbuktu mai tarihi.

Majiyoyin sojojin kasar Mali sun ce dakaru sun isa yankin Timbuktu ba tare da sun ci karo da wata turjiya ba.

Dadadden birnin wanda ke yankin hamada na cikin muhimman wuraren tarihin da asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ya ware, har wa yau wuri ne mai dimbin Masallatai da kuma hubbaren karrama waliyai na zamanin da.

A farkon wannan wata Faransa ta kaddamar da harin soji a Mali bayan da ‘yan tawayen da suka kama akasarin arewacin kasar a bara, su ka fara dannawa zuwa Bamako babban birnin kasar.‘Yan tawayen sun kafa tsarin mulkin shari’ar Islama tsantsa a yankunan da ke karkashin ikon su, kuma sun yi ta yanke hukunci mai tsanani a kan fararen hular da ba su bi dokar ba.
XS
SM
MD
LG