Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Adawar Masar Zata Ci Gaba Da Zanga-Zanga


Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.
Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.
Babbar kungiyar yan adawar Masar, The National Salvation Front, za ta ci gaba da da shirin yin zanga-zangar nuna adawar ta ga gwamnati a fadar shugaban kasa da ke al-Qahira yau jumma’a.

Manyan shugabannin yan kungiyar adawa sun yi kira ga shugaba Mohammed Morsi da ya kafa hadadiyar gwamnatin kasa wadda zata basu damar shiga majalisa.

Magoya bayan Mr. Morsi sun ki su amince da wannan rokon, akan cewar yan adawar na kokarin samun iko ne kawai wanda baza su iya samu ba ta hanyar zabe.

Jiya alhamis yan siyasar isalama da masu sassaucin ra’ayi sun yarda su bar rikici su kuma shiga cikin tattaunawar kasa da za ayi da kudurin kawo karshen mummunan rikicin da ake yi a kasar na tsawon watanni.

Sheik Ahmed al-Tayeb babban malamin addinin islama, shine ya shugabnci taron da aka yi a helkwatar yan sunni a alkahira, wato al-azhar.

Ya fadawa wakilan bangarorin siyasar kasar da ke gaba, cewa hanya daya ce kawai za a iya magance banbance-banbancen da ke tsakanin su itace ta hanyar ba da damar tattaunawa ga kowa.
XS
SM
MD
LG