Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kaiwa Masallacin Shi'a Farmaki


Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake.
Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake.
Jami’ai a arewa maso gabashin Pakistan sun ce wani dan kunar bakin wake ya kai farmaki a masallacin yan shi’a, inda ya kashe akalla mutane 19, fiye da 30 kuma suka raunata.

Hukumomi sun ce fashewar bam din da ya faru a birnin Hangu ya faru ne yayinda yan shi’a suka gama sallar jumma’a suke barin masallacin, amma wadanda abin ya rutsa da su sun hada yan sunni da ke a masallacin da ke kusa da na yan shi’ar.

Birnin Hangu dai dama wuri ne da aka fi yawan tashin hankali musamman fada da yan shi’ar da basu da rinjayi, wadanda sune kashi 20 bisa dari din yan Pakistan. Mayakan sa kan sunni sun dauki yan shi’a a matsayin wadanda ba sa bin cikakken koyin addinin.

Har Yanzu dai ba a sami wanda ya dau alhakin kai harin ba.

A halin da ake ciki kuma kafar yada labaran turkiyya ta bada ruhoton fashewar bam a wajen ofishin jakadancin Amurka a Ankara ya kashe mutum daya.

Har Yanzu ba a iya sanin dalilin wannan fashewar bam din ba.

Motocin yan kwana-kwana da na asibiti sun je wurin don aikin agajin gaggawa.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG