Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Benedict Zai Yi Sallama Ga Darikar Katolika Ranar 27 Ga Fabrairu


Taageerayaasha xulka Brazil oo la ilmeyay guuldaradii xulka Brazil
Taageerayaasha xulka Brazil oo la ilmeyay guuldaradii xulka Brazil
Wani kakakin fadar Vertican yace Paparoma Benedict zai yi sallama ga darikar Katolika a bainin jama’a ranar 27 ga watan nan na Fabrairu, kwana daya kafin ainihin ranar da zai yi murabus.

Kakakin fadar Vertican Federico Lombardi ya shaidawa manema labarai yau Talata cewa, Paparoma zai yi sallama ranar 27 a dandalin taron na St. Peters. Fadar ta Vertican ta kuma bayyana cewa, tana kyautata zaton za a zabi sabon Paparoma kafin ranar Esta-31 ga watan Maris.

Paparoma Benedict ya ba duniya mamaki da tare da sanarwar bazata ta yin murabus jiya Litinin. Shugabannin darikar zasu zabi sabon shugaba bayan saukar Paparoman.

Paparoman dan asalin kasar Jamus mai suna Cardinal Joseph Ratzinger, yace zai yi murabus ne sabili da tsufarsa tasa gudanar da ayyukansa suna zamar mashi da wahala.

Yau talata karon farko fadar Vertican ta bayyana cewa, Paparoman yana amfani da wata na’urar kara mashi karfi, Lambardi yace an sa mashi na’urar ne wani lokaci da ya shige, kuma an sake batirinta watanni uku da suka shige.

Paparoma Benedict shine paparoma na farko da yayi murabus daga mukamin tun shekara ta dubu da dari hudu da goma sha biyar, lokacin da Paparoma Gregory ya sauka daga mukamin domin warware takaddama da ake yi kan shugabanninci darikar mai membobin miliyan dubu dari da biyu a duk fadin duniya.

Jami’an fadar Vertican sun bayyana yau Talata cewa, Paparoma Benedict bashi da niyar tsoma baki kan zaben wanda zai gaje shi.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG