Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Karin Kudi Domin Yaki da Cutar Sikari da Hawan Jini a Nigeriya


Ana jegon mai fama da ciwon suga
Ana jegon mai fama da ciwon suga

Wani dan Majalisar dattawa na Nigeriya, Senato Lee Maeba, ya kalubalanci gwamnatin tarayya domin su maida hankali sosai wajen lura da kokarin kawarda cutar sikari musamman domin gwaji da yin magani.

Wani dan Majalisar dattawa na Nigeriya, Senato Lee Maeba, ya kalubalanci gwamnatin tarayya domin su maida hankali sosai wajen lura da kokarin kawarda cutar sikari musamman domin gwaji da yin magani.

A madadin karuwar kira domin karin tanada kudin neman maganin cutar kanjamau, an roki gwamnatin tarayya ta juya tanajin kudinta ga sauran cututtuka kamar su kanjamau da ake maida hankali sosai gare shi fiye da cututtuka kamarsu cutar sikari da cututtukan zuciya.

Dan Majalisar Lee Maeba ya bada wannan gargadin a farkon yin bincike na kyauta na cutar sikari wanda wannan kungiyar tayi, Dan Majalisa Lee Maeba da sukayi aikin hadin hannu na wannan kungiyar hadi da ma’aikatar lafiya ta tarayya a Abuja.

Tunda wuri, ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu yace ma’aikatar tana hada hannu da kungiyoyi nagari domin rage wannan cutar ta sikari.

Yayi bayanin cewa fiye da kashi uku na yawan mutuwar wannan cutar sikarin ta faru ne a kasashe masu fama da talauci hadi da Nigeriya.

Dan Majalisa Lee Maeba ya gargadi ‘yan Nigeriya su kauce daga wannan cutar tawurin cin abinci mai nagari, rage shan giya, kauda shan taba, motsa jiki yadda ya kamata da kuma rage shan sikari.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG