Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashen Hausa Zai Yi Karin Lokacin Shirin Safe Daga Ranar 31 Ga Watan Oktoba


Sashen Hausa na Muryar Amurka zai kara tsawon lokacin gabatar da shirinsa na safe mai farin jini zuwa sa'a daya cur tun daga ranar litinin 31 ga watan Oktoba, 2005.

Da yake bayyana musabbabin karin lokacin, shugaban Sashen hausa, Sunday Dare, ya ce dimbin wasikun masu sauraro da aka yi ta samu cikin shekarun da suka shige na neman karin lokaci, kuma ganin cewa an fi sauraron shirin na safe fiye da kowanne, ya sa aka yanke shawarar wannan karin lokaci.

Shugaban ya ce wannan karin lokaci, da farko, zai shafi shirye-shiryen safiyar litinin zuwa jumma'a ne, inda za a ringa bude tasha tun daga karfe 5:30 na safiya agogon Nijeriya da Nijar domin masu sammako.

Mr. Dare ya ce sabon shirin sa'a daya da safe zai kunshi karin labarai da dumi-duminsu daga Nijeriya, Ghana, Nijar da Kamaru daga wakilan da Sashen ya baza cikin wadannan kasashe.

Har ila yau, sabon shirin na tsawon sa'a daya da safe zai kunshi karin labarai da rahotanni daga kowane lungu na duniya da kuma rahotanni na musamman kan batutuwa kamar siyasa, addini, noma, kiwon lafiya da sauransu.

Haka kuma kuma akwai wakokin gargajiya na Hausa, kamar wakoki irin na Mamman Shata, Musa Dan Kwairo, Dan Anache, Salisu Jankidi, Ahmadu Doka, da sauransu.

Za a kuma fadada karanto wasikun masu sauraro, tare da gabatar da sharhin jaridun kasashen Afirka kamar na Nijeriya, Nijar da Ghana.

Idan aka bude tasha da karfe 5:30 na safiya agogon Nijeriya, da farko za a kama mu a kan mitoci uku: 49 (kilohaz 6015), Mita 41 (Kilohaz 7290) da kuma Mita 31 (Kilohaz 9885). Da zarar karfe 6 na safiya yayi kuma, za a yi karin mitoci biyu a kan guda uku na farko, watau za a ji mu a kan Mita 195 (Kilohaz 1530 MW) da kuma kan Mita 60 (Kilohaz 4960).

XS
SM
MD
LG