Talata, Mayu 26, 2015 Karfe 16:38

Afirka

A Mali Sojojin Kasar Cadi Sun Fara Shiga Birnin Kidal

Sojojin kasar MaliSojojin kasar Mali
x
Sojojin kasar Mali
Sojojin kasar Mali
Sojojin daga Cadi sun fara shiga birnin Kidal, tungar karshe da ta rage hanun mayakan sakai masu ikirarin islama, kamin dakarun Faransa  da Mali su kama birnin.

Yau talata jami’an Farans a suka  ce kimanin sojojin Cadi dubu daya da dari takwas(1,800) sun fara shiga birnin. Wannan mataki yazo ne mako daya bayanda sojojin Mali da Faransa ta yiwa jagoranci, suka kama tashar saukar jiragen sama dake birnin.

Ma’aikatar tsaron Faransa ta fada cewa ta kai hare hare ta sama har 25 kan wasu muradun mayakan sakai masu ikirarin Musulunci cikin ‘yan kwanakin nan.

Faransa  wacce ta kaddamar da shirin kutse a mali cikin watan jiya, ta bada sanarwar zata fara janye sojojinta sannu a hankali ta mika biranen da ta ‘yanto zuwa ga sojojin Mali da dakarun daga nahiyar Afirka.

Ranar litinin, jami’an Faransa suka bada sanarwar fara janye galibin sojojinta daga shahararren birnin nan na Timbuktu.

A wani cigaba, kungiyoyin kasa da kasa da jami’ai daga Mali suna taro talatan nan  a binrin Brussels domin tattaunawa kan hanyoyin sake daidaita al’amura cikin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, data Afirka, da k,ungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka watau ECOWAS  suna daga cikin wakilai kusan 45  da suke halartar taron.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti