Alhamis, Nuwamba 26, 2015 Karfe 16:56

Labarai / Sauran Duniya

Shugaba Morsi ,Ya Ayyana 15 Ga Disemba Domib Kuri'ar Raba Gardama.

Shugaban Masar Mohammed Morsi.Shugaban Masar Mohammed Morsi.
x
Shugaban Masar Mohammed Morsi.
Shugaban Masar Mohammed Morsi.
Aliyu Imam

Shugaban Masar Mohammed Morsi ya ayyahna ranar 15 ga watan Disemba domin a yi zaben kuri’ar raba gardama kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar, wanda  ya janyo rarrabuwar kawuna da kuma zanga zanga masu karfi.

shugaba Morsi ya ayyana ranar ce, bayanda wakilan majalisar  da ta rubuta tsarin mulki wacce masu ra’ayin addini suka mamaye ta, suka mika masa kofin daftarin a daren Asabar.

Daftarin tsarin mulkin bai canza manufofin kasar na dogaro kan tafarkin  Islama a matsayin hukunce hukuncen kasar.

Tunda farko a jiya Asabar, dubun dubtan ‘yan kasar masu goyon bayan tafarkin addini suka yi zanga zangar nuna goyon bayansu ga shugaba Morsi d a kuma sabon daftarin tsarin mulkin. Gungun mutanen sun hallara ne a harabar jami’ar Alhakira d a kuma a wasu wurare suna kada tutoci, da kellaye da hotuna suna neman a aiwatar da abund a suka kira “dokokin Allah.” Kungiyar da ake kira ta “Yak u ‘yan ‘yan uwa musulmi ne ta shirya gangamin.
A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.
x
A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.
A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.

Haka ma a jiya Asabar din dubban ‘yan Masar din ne suka yi zanga zanga a wuni na tara a jere a dandalin Tahiri domin nuna adawa kan shugaba Morsi da  kuma sabon daftarin tsarin
'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir
x
'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir
'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir
mulkin kasar.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Idris Abubakar Daga: Zaria
04.12.2012 11:51
Lallai mutanen kasar masar wasu sun fahimci inda aka saka gaba wasu kuma basu fahimata lallai shugaba Mursi abinda da kayi shine dai dai Allah yakara maka jagora amin

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye