Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai a Sudan Sun Yi Zanga-Zanga Akan Cibok


Dalibai a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Bayan, a birnin Khartoum dake Sudan suna kira a nema dalibai mata da aka sace a Cibok. Mayu 2, 2014
Dalibai a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Bayan, a birnin Khartoum dake Sudan suna kira a nema dalibai mata da aka sace a Cibok. Mayu 2, 2014

A wani al'amari mai nuna dan'uwantaka tsakanin matasan kasa da kasa, a Sudan daliban Jami'a sun yi zanga-zangar neman a maido da dalibai matan da aka sace a garin Chibok na Jihar Borno

A cigaba da yaduwar kururuwar neman a maido da dalibai 'yan matan da aka sace su a garin Chibok na jihar Borno, daliban Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Bayan, a birnin Khartoun, Sudan sun yi zanga-zangar kiran hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen daukar matakan kubuto 'yan matan.

Wani mai magana da yawun daliban mai suna Fahd Abbas Jega, ya shaida ma abokin aikinmu Bello Habib Galadanchi cewa tausayi da dan'uwantakar da ke tsakanin daliban ne dalilinsu na mara ma takwarorinsu 'yan asalin Nijeriya wajen yin wannan zanga-zanga ta lumana.

Ya ce dalibai 'yan Nijeriya sun kadu sosai da jin labarin sace dalibai mata a makarantar Chibok a jihar Borno; don haka sai su ka yanke shawarar shirya wannan zanga-zangar lumana da hadin gwiwar wasu dalibai 'yan asalain kasashen Masar da Sudan na bukatar a maido da daliban da aka sace a Nijeriya.

Malam Fahd ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zangar ce bisa shawarar Shugaban kungiyar daliban Nijeriya na Kwalejin mai suna Faisal Abdullahi Jaram. Wasu daga cikin kwalayen da su ka daga na dauke da sakon cewa, "A Maido Ma Na Da Dalibai Mata 'Yan'uwanmu." Baya ga daga kwalayen, zanga-zangar ta kuma hada da yada wannan bukatar a dandalin sada zumunci na intanet don a sani sosai.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG