Litinin, Mayu 25, 2015 Karfe 20:24

Afirka

A Zambia Hadarin Mota Ya Kashe Fiye Da Mutum 50

Taswirar Zambia.Taswirar Zambia.
x
Taswirar Zambia.
Taswirar Zambia.
‘Yansanda a Zambia sun ce akalla mutane 51 sun mutu lokacinda wata motar Bas  dauke fasinjoji masu yawa tayi karo da wata babbar motar mai dakon kaya.

Alhamis din nan motocin biyu suka yi karon kan wata babbar hanya kimanin kilomita 100 daga arewacin babban birnin kasar Lusaka.

Kakakin rundunar ‘Yansanda Elizabeth Kanjela, tace yawan wadanda suka halaka a hadarin yana iya karuwa domin masu aikin ceto suna neman gawarwakin da baraguzan motocin biyu suka daddanne su.

Hukumomin kasar suka ce babu bayanai da  suka samu nan da nan kan musabbabin wannan hadari.

‘Yansanda suka ce motar fasinjar ta hukumar gidan woyar Zambia, wacce tana dibar fasinja banda aikin raba wasiku.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti