Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abati Yace Su Na Tattaunawa Da Kungiyar Boko Haram


Wakilan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Amurka ke yin gargadi game da yiwuwar wani harin da za ta kai kan manyan otel-otel din da Turawa ke sauka a Abuja.
Wakilan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Amurka ke yin gargadi game da yiwuwar wani harin da za ta kai kan manyan otel-otel din da Turawa ke sauka a Abuja.

Kakakin Shugaba Goodluck Jonathan, Reuben Abati, yace ana tattaunawar “bayan fage” domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa

Wani kakakin shugaban Najeriya ya tabbatar da cewa da gaske ne gwamnati tana tattaunawa da kungiyar Boko Haram, wadda aka dora wa alhakin kisan daruruwan mutane.

Kakakin shugaban, Reuben Abati, yace ana tattaunawar “bayan fage” domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a yankin arewacin Najeriya inda tashin hankalin ya fi tsanani.

Abati ya fadawa ‘yan jarida jiya lahadi a Abuja cewa gwamnati tana son ta fahimci irin koke-koken da kungiyar ke da su domin ta iya kawo karshen wannan tashin hankali. Amma kuma yace gwamnati zata dora ma duk wanda ya keta doka alhakin hakan.

Wannan furuci na Reuben Abati, shi ne karon farko da wani jami’in gwamnati ya fito fili yace Najeriya tana tattaunawar neman yin sulhu da kungiyar Boko Haram.

A baya cikin wannan watan ne wani mutumin dake ikirarin cewa shi mai magana da yawun kungiyar ne ya fadawa Muryar Amurka cewa su na tattaunawa da gwamnati a saboda rokon da jama’a ke yi na ganin an yi sulhu.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG