Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adu'a Na Masamma Domin 'Yan Matan Chibok a Amurka


Adua ta masamma a kofar ofishin jakadanci Najeriya a Washington DC.
Adua ta masamma a kofar ofishin jakadanci Najeriya a Washington DC.

Yau anyi gangami na adua a kofar ofishin jakadancin Najeriya dage birnin Washington DC.

Gamayya Kungiyar kare muradun mabiya addini krista na Amurka yau sunyi gangami na adua a kofar ofishin jakadancin Najeriya dage birnin Washington DC.

Shugaban kungiyar Rev. Patrick Mahoney, yayi amfani da wannan damar yayi kira ga shugaban Amurka Barack Obama, da yayi amfani da karfin kujerasa da kuma kimiyar zamani da Amurka, ke dashi domin gano da kuma kubutar da ‘yan matan Chibok da aka sace.

Rev.Mahoney,ya kara da cewa yau wata daya har yanzu babu wani mahimmin labari na inda ‘yan matan suke.

Yace tunda Amurka ta iya kama Osama Bin Ladin,bai ga dalilin da zai sa,kungiyar Boko haram,ta gagari Amurka ba.

Ita kuwa a cikin nata jawabi a wuri gagamin aduar Dr. Anthonia Umeh, Shugabar kungiyar mata ‘yan asalin jihar Anambra,a Najeriya, amma mazauna kasar Amurka, kira tayi ga hukumomin Najeriya dasu tabattar da tsaro ga ‘yan makarata duk a fadin Najeriya.

Tace duk inda ake rikici a duniya mata da yara ke shan wahala,saboda haka ya zama wajibi ga gwamnatoci duniya, su tabbatar da tsaron yara da mata a duk fadin duniya.
XS
SM
MD
LG