Asabar, Mayu 30, 2015 Karfe 21:26

Afirka

Afirka Ta Kudu Ta Tura Sojojin Kasar Su 400 Zuwa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.

Central African Republic President Re-ElectedCentral African Republic President Re-Elected
x
Central African Republic President Re-Elected
Central African Republic President Re-Elected
Aliyu Imam
Ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta kudu tace tura sojojin ya nuna cewa Afirka zata iya magance matsalolinta ba tare da tsoma hanun wasu daga waje ba.

A maraicen lahadin nan ne ofishin shugaban kasar Afirka  ta kudu ta bada sanarwar tura sojojin, da tace ta yi tun cikin makon jiya. Sanarwar da Afirka ta kudun ta bayar, tace sojojin zasu taimakawa sojojin kasar Afirka ta tsakiya su kare farmakin da ‘yan tawayen  da  suke dannawa kan birnin Bangui, wadanda yanzu suke kasa da kilmita metan daga birnin.

Wannan bore na baya bayan nan, yana  daya daga cikin irinsu masu yawa da suka addabi wannan kasa mai fama da kuncin talauci, duk da  arzikin albarkatun kasa da Allah ya bata, tun lokacin da ta sami ‘yancin kai daga kasar Faransa a 1960.  Shugaban kasar na yanzu ya hau mulki ne a 2003 bayan juyin mulki, amma daga bisani yayi takara aka zabe shi kan wannan mukami.

Sanarwar da ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ta bayar, tace sojojinta zasu ci gaba da kasancewa a  jamhuriyar Afirka ta tsakiya har zuwa 2018, inda  zasu taimaka wajen sake gine rundunar mayakan kasar, kuma za su taimaka wajen kwance damarar ‘yan tawaye, da sake daukar su cikin rundunar mayakan kasar.

Afirka ta kudu tana cikin kasashe masu yawa da suka tura sojoji zuwa Afirka ta tsakiya, da nufin kare gwamnatin kasar daga gamayyar ‘yan tawaye da ake kira Seleka, wadanda tuni suka kama kamar sulusin kasar.

Daya daga cikin korafe-korafen ‘yan tawayen na Seleka, sun hada da  cewa gwamnatin kasar ta gaza cika alkawura  da  ta dauka, ciki harda kwance damar ‘yan tawayen  da sake taimaka musu su zauna cikin jama’a. Amma wasu ‘yan tawayen suna bukatar ‘shugaban kasar ya yi murabus, abinda gwamnatin tace ba  zata sabu ba.

‘Yan tawayen sun yi alkawarin  za  su halarci shawarwarin sulhu da aka shirya a wani lokaci cikin makon nan, a Gabon. Amma masu nazari suna shakkar ko akwai hadin kai tsakanin ‘yan tawayen, da zai kai su ga cika alkawarin.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti