Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Fahintar Juna Tsakanin Najeriya Da Cameroun Game da Batun Bude Dam.


A tataunawar da Mamud Lalo yayi da Barister Abdullahi Dan Wanka na cewa ko akwai wata doka game da wannan sako ruwan da kasar Cameroon zata yi wanda zai shigo Najeriya? Sai ya amsa da cewa.

Babu wani abu da akayi illa anyi yarjejeniya ta kawance wadda ake kira da turanci MEMORANDUM OF UNDERSTANDING (MOU) tsakanin gwanmnattin Najeriya dana Cameroon, kuma wannan yarjejeniyar kusan abubuwa ukku ne tayi Magana akai, abubaun ko sune, za a umurci dukkan wadanda zasu iya shafuwa da wannan matsalar idan an bude wannan dam da su bar garuruwan da suke, ko kuma su matsa sabo da idan an bude wannan dam din kar su samu wannan matsalar,Idan hali ya kama kuma a dauke su a canza musu garuruwa to za ayi hakan, sai kuma za a inganta harkoki sadarwa tsakanin gwamnatin Najeriya dana Cameroon.

Haka kuma idan ta kama za a kara kawance na kwararru na kasashen guda biyu domin shawo kan wannan matsalar to kuma tun daga lokacin wannan kawnce da aka kulla tun daga wannan lokacin kawo yanzu ba wani abu da ya biyo baya akan wannan maganar .

Mamud yace masa Kenan tunda kasar ta Cameroon ta sanar da Najeriya zata bude wannan ruwan ace ta wanke kanta,Kenan ya rage ga hukumomin Najeriya ta dauki matakan da ya kamata? Anan ko ga abinda ya amsa.

Eh! Ace ta wanke kanta ace bata wanke kanta ba domin a wancan karo da aka samu matsala da aka wanke dam, su kan kansu kasar Cameroon din ruwa yayi musu banna, domin kamar shi yadda kwamishinan harkokin ruwa da makamashi Dr Bezi Atangana Kwana yace a kalla akwai mutane kusan dubu 40 da suka rasa gidajen su ko gonakin su sakamakon wannan ambaliyar ruwa.

Tunda Gwamnatin Cameroon tasan wannan abin akwai illa, bada sanarwan zata bude kadai bai wadatar ace wai ta wanke kanta ba, tunda zai cutar dasu muma zai cutar damu.

Sai dai har wayau Mamud yace masa to ai sunce zasu sanar kamar yadda kayi bayani a baya.

Duk da haka gaskiya akwai bukata daga bangaren gwamnatin Najeriya a dauki mataki na gaggawa kafin gwamnatin Cameron ta bude wadannan dam,kuma abinda ya dace shine kodai a duba wannan yarjejenyar aga wane gyara za ayi mata domin a hana bude wannan ruwa domin gwamnatin Cameroon din da dauki matakin yadda koda ta bude mu ba zai cutar damu ba, lallai mu akwai wannan bukata mu a bangaren mu.

Ga cikakkiyar hirar tasu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG