Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutane dari da saba'in a kasar Malawi


Yara a cikin ambaliyar ruwa a kasar Malawi
Yara a cikin ambaliyar ruwa a kasar Malawi

Jami'an kasar Malawi sunce ambaliyar ruwa ta kashe akalla mutane dari da saba'in da shidda, kuma ana tsumayen karin ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin makoni biyu zuwa makoni uku masu zuwa. Jiya Juma'a mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima yace tana yiwuwa yawan mutanen da suka mutu ya karu, domin an bada rahoton cewa akwai mutane da dama da suka bace.

Jami'an kasar Malawi sunce ambaliyar ruwa ta kashe akalla mutane dari da saba'in da shidda, kuma ana tsumayen karin ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin makoni biyu zuwa makoni uku masu zuwa.
Jiya Juma'a mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima yace tana yiwuwa yawan mutanen da suka mutu ya karu, domin an bada rahoton cewa akwai mutane da dama da suka bace. Yace yankunan da akl'amarin yafi muni an kasa kaiwa gare su, domin ambaliyar ruwa tayi awon gaba da hanyoyi da kuma gada.
Gwamnatin kasar Malawi ta bukaci taimakon kasa da kasa, kuma ta ayyana gudumomi ashirin da takwas na kasar a zaman yankunan bala'i.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, ambaliyar ruwa a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kwanaki ana yi, ta tilastawa mutane dubu dari da goma ficewa daga gidajensu.
Shirin samar da wadatar abinci na Majalisar yace zai yi jigilar fiye da ton dari na biskit dake kunshe da kayayyakin gina jiki sosai, domin biyan bukatun wadanda ambaliyar ta yiwa barna.
Shugaban shirin bada taimako na kungiyar na gari na kowa, Doctor Without Boarders a kasar Malawi, Amaury Gregoine yace ambaliyar tana da dan kamar tsunami, domin rafi ya cika ya batse.
Shirin yace ya damu, domin mutane da suka rasa matsuguninsu, suna fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka a saboda rashin tsaftace muhalli.
Hukumomin sun baiyana tsoron kila a samu bular anobar kwalera a yankunan kudancin kasar, inda ruwan sama kamar ta bakin kwarya ta lalata hectocin hatsin da aka shuka..
Kasar Mozambique makwapciyar Malawi, itama tayi fama da matsalar ruwan sama kamar da bakin kwarya. Kamfanin dilancin labarun kasar da ake cewa AM a takaice ya bada labarin cewa akalla mutane talatin da takwas ne suka mutu a kasar a sakamakon ambaliyar ruwa.

XS
SM
MD
LG