Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Kwashe Fursunonin Dake Guantanamo


U.S. President Barack Obama
U.S. President Barack Obama

Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fara gwada ingancin wani sansanin soji a Leavenworth na jahar Kansas, don yiwuwar kai fursunonin soji, wadanda a yanzu ke gidan yarin Guantanamo Bay, na kasar Cuba

Sansanin na Leavenworth da wani sansanin sojin kuma da ke Charleston, na Jahar South Carolina su ne wurare biyu da Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya ba da umurnin a gwada ingancinsu, a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar ta Tsaro. Yayin da jami'an sojin su ka fara gwada dacewar sansanin na Leavenworth jiya, shi kuwa na Charleston sai sati mai zuwa, a bayanin da jami'in ya yi ma Muryar Amurka.

Ana bukatar kai 50 daga cikin fursunonin a sansanin da ke Amurka, a cewar wani jami'in Ma'aikatar Tsaron Amurka. A yanzu haka akwai fursunoni 116 a gidan yarin Sansanin Sojin Ruwan Guantanamo Bay. Da yawa daga cikinsu kuma sun cancanci a kai su wasu kasashen.

Jami'in ya ce jami'an sojin za su kuma duba yiwuwar gwada wasu karin sansanonin soji da na farar hula, don sanin ko za a iya kai fursunonin soji a wuraren cikin abin da ya kira "yanayi na mutunci da tsaro."

Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron ta Pentagon Capt. Jeff Davis ya fadi a farkon wannan satin cewa da yiwuwar Ma'aikatar ta Pentagon ta mika ma Majalisar Tarayyar Amurka tsarin shirin rufe gidan yarin Guantanamo Bay wani lokaci bayan Majalisar ta dawo daga wani hutun Agusta.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG