Alhamis, Nuwamba 26, 2015 Karfe 01:14

Labarai / Afirka

Amurka Ta kafa Sansanin Jiragen Yakinta Maras Direba A Nijar.

Samfirin jirgin yaki da bashi da matuki.Samfirin jirgin yaki da bashi da matuki.
x
Samfirin jirgin yaki da bashi da matuki.
Samfirin jirgin yaki da bashi da matuki.
Jami’an tsaron Amurka sun ce Washington ta tura jiragen yakin da basu da matuka zuwa Nijar, domin aikin leken asiri, da nufin taimakawa sojojin Faransa da suke fafatawa da ‘yan gani-kashenin Islama a Mali dake makwabataka da Nijar din.

Jami’an tsaron Amurka da aka ambata a kaofinnyada labarai dake nan Amurka sun ce jiragen da  basu da matuka za a girke su ne kusa  da Niamey babban birnin kasar ta Nijar, tare da sojojin sama na AMurka kamar su dari.

A cikin wasika sanar da majalisar dokokin Amurka da ya aike wa wakilai jiya jumma’a, shugaba Obama yace za a yi amfani da jiragen ne wajen tara bayanan sirri. Shugaba Obama bai fito fili cikin wasikar ya bayyana kasar da za a girke jiragen ba, amma jami’an sojin Amurka da suka yi magana bisa sharadin ba  za a bayyana sunayensu ba, sun ce galibin dakarun Amurka da suka isa Nijar ranar laraba, mayakan sama ne da zasu yi aiki domin tallafawa jiragen da basu da matuka.

Amurka da turai sun bayyana damuwar cewa mayakan sakai na kungiyar al-Qaida suna kokarin fadada ikonsu ta wajen wasu sassan yammacin Afirka barazana ga tsaron kasashen duniya.

Watakila Za A So…

Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shrin Safe

Shrin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye