Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sa Tukuicin Dala Miyan Biyar Kan Al-Shamali


John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka
John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Amurka ta bada tayin tukuicin dala miliyan biyar ga labarin da zai kaiga kama Al-Shamali na kungiyar ISIS.

Amurka tana tayin zata bada tukuicin dala milyan biyar, ga duk wanda zai bata bayanai da zasu kai ga kama wani shugaban kungiyar ISIS mai suna Abu Mohammed al-Shimali.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace Al-Shimali ne mai shirya wa mayakan sakai hanyoyin zuwa Syria daga Turkiyya domin shiga cikin kungiyar ta ‘yan yakin sa kai.

Hukumomi sun hakikance da cewa shine yake kula da "ayyukan sumogal, da aikewa da kudade, da kuma jigilar kayayyaki zuwa Syria da Iraqi da aka kawo daga Turai, da Afirka ta yamma, da kuma zirin Arabiya. Kamar dai yadda sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta baiyana.

XS
SM
MD
LG