Alhamis, Satumba 03, 2015 Karfe 18:10

Labarai / Sauran Duniya

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya ya sauka daga karagar mulki

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, bayan zargin yiwa wani shugaban hamayya kisan gilla.

Wata mace cikin masu zanga zanga dauke da tutar kasar Siriya.
Wata mace cikin masu zanga zanga dauke da tutar kasar Siriya.

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, bayan zargin yiwa wani shugaban hamayya kisan gilla.

Sanarwar Fadar White House ta kushe da kakkausar murya,  kisan Mashaal Tammo, kakakin jam’iyar makomar Kurdawa da aka fi sani da suna Kurdish Future Party, kuma memban sabuwar kungiyar hamayya ta hadin guiwa a Siriya. ‘Yan gwaggwarmaya sun ce wadansu ‘yan bindiga da suka rufe idanunsu ne suka kashe shi a gidanshi dake garin Qamishli a arewacin kasar jiya Jumma’a.

Fadar White House tayi gargadi da cewa, tilas ne Mr. Assad ya sauka daga karagar mulki yanzu, kafin ya kara jefa kasar cikin yanayi mai hadari.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, hare haren  sun nuna yunkurin gwamnatin kasar Siriya na baya bayan nan na murkushe hamayyar lumana da ake yi a Siriya, inda dubban masu zanga zanga suke taruwa domin nuna kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Shugaban adawan yana daga cikin mutane takwas da ake zargin jami’an tsaro da kashewa jiya jumma’a a Siriya,

Tun farko shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev yace Mr. Assad yana bukatar yin garambawul ko kuwa ya yi murabus. Sai dai ya kara da cewa, Rasha tana adawa da yunkurin kasashen ketare na kauda Mr. Assada daga karagar mulki.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti