Laraba, Nuwamba 25, 2015 Karfe 05:10

Labarai / Sauran Duniya

Amurkawa Suna Matukar Bakin Cikin Kisan Da Aka Yi A Makaranta

Yan makaranta suna fita daga inda aka yi harbe harbe
Yan makaranta suna fita daga inda aka yi harbe harbe
Daruruwan masu makoki sun taru a  majami’a a garin Newtown, jihar Connecticut jiya jumma’a da dare domin jimamin rashin kananan yara 20 da kuma wadansu mutane shida da wani dan bindiga ya kashe a wata makarantar firamare.

Hotunan talabijin sun nuna daruruwan masu makoki a waje bayan wadanda suke cikin majami’ar da ta cika makil, yayinda al’ummar ke binbinin bala’in da ya faru. Gwamna Dannel Maloy ya bayyana cewa, “mugun abu ya ziyarci wannan al’ummar yau”.

Tun farko a Washington, Shugaban Amurka Barack Obama cikin matukar bakin ciki yana kwalla, ya yi jawabi ga Amurkawa, inda ya bayyana jimamin rashin ya kuma ce tilas ne kasar ta dauki matakin kawo karshen irin wannan tashin hankalin.

Wannan kasa tamu ta fuskanci irin wannan masifa sau da dama a baya, ko a makarantar firamare ta Newtown, ko harbin kan mai uwa da wabi a jerin kantunan Oregon, ko a wurin ibada a Wisconsin, ko kuma a gidan silma a Aurora, ko a kan tituna dan birnin Chicago, wadannan duka unguwanninmu ne, kuma wadannan yaran, yaranmu ne. Kuma tilas ne mu hada kai mu dauki matakin hana ci gaba da aukuwar irin wannan bala’in, ko da menene ra’ayin siyasarmu.

Shaidu sun ce mutumin dan shekaru 20 da haihuwa sanye da bakaken tufafi  da kuma rigar kare harsashe irin ta soja, ya shiga makarantar firamaren da safe ya budewa kananan yara wuta da malamansu a zuzuwa biyu. An sami wata bindiga irin ta sojoji a motarsa daga baya. Mutumin mai suna Adam Lanza ya kashe kansa, aka kuma sami wadansu kananan bindigogi biyu kusa da shi.

An gudanar da addu’oin tunawa da mamatan a birane da dama a duk fadin kasar.

Hukumomi sun ce, dan bindigar ya kashe mahaifiyarsa a gidanta kafin ya tuka motarsa zuwa makarantar.

Yan sanda basu tabbatar da masababin kashe kashen ba.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye