Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tahir Monguno Ya Tabbatar da Auren Daliban Cibok


Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna maida jawabi a taron da suka yi da gwamna jihar Borno, a Chibok, har wasu na kuka.
Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna maida jawabi a taron da suka yi da gwamna jihar Borno, a Chibok, har wasu na kuka.

Yayin da aka share makonni uku da sace dalibai mata a makarantar Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, wani dan Majalisar Wakilai ya tabbatar cewa 'yan bindigar sun fara auren 'yan matan.

Mai wakiltar mazabun Marte da Monguno da Nganzai a Jihar Borno, a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhaji Muhammad Tahir Monguno, yace tuni har 'yan bindiga sun fara auren dalibai 'yan mata da su ka sace su a wata makaranta a garin Chibok na jihar Borno..

Ya ce ya sami labarain cewa kwanaki hudu da su ka gabata 'yan bindigar sun yi bikin auren wasu daga cikin 'yan matan a wani kauye mai suna Wafa da ke karamar Hukumar Ajiri sannan suka yi gaba da su.

Monguno ya kara cewa Wafa na da tazarar kilomita 70 daga Maiduguri.

Honorabul Tahir ya ce kuma an gaya masa cewa cikin kwanaki uku da su ka gabata an ga wasu daga cikin 'yan matan a wani kauye mai suna Shuwaram, wanda bashi da nisa sosai daga Monguno kuma har an shaida ma jami'an tsaro.

Honorabul Tahir ya shaida wa Bello Habeeb Galadanchi na Sashen Hausa a Muryar Amurka ta wayar tarho cewa ba'a wuri guda aka tafi da 'yan matan da aka sace din ba; an raba su ne wurare daban-daban.

To sai dai Tahir ya tabbatar wa Bello cewa sojoji sun bazu a daji neman 'yan matan sai dai kawai suna taka tsantsan kar kokarin kubutar da su ya janyo masu hallaka su.

Daliban mata su 234, ‘yan ajin karshe ne dake rubuta Jarrabawar Fita daga Sakandare a Yammacin Afirka, ko WAEC a takaice a lokacin da ‘yan bindiga suka kaiwa makarantarsu farmaki cikin daren Litinin, sama da makonni biyu kennan, inda suka kona makarantar mallakar gwamnati baki dayanta, sannan suka kwashe daliban a cikin manyan motoci suka tafi dasu.

Hukumar tsaron Najeriya, ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye da hukumomin makaranta suka musanta, kuma daga baya hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu dai bata sake bayanna wani mataki ko daya ba, akan irin aikin da takeyi na gani ta ceto daliban.

Shugaba Jonathan ya gudanar da taro Alhamis dinnan da duka gwamnoni, da shuwagabannin al-umma, da hukumomin tsaro game da batun tsaro, inda taron ya kayyade da bayanna matakai da za'a dauka domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Iyaye da ‘yan uwan daliban sun yi kokari da kansu su ceto matan, ta hawa babura sama da 150 domin bin sawun ‘ya’yansu, amma an gargade su akan cewa mutanen da suka sace daliban na dauke da makamai. A farkon makonnan ne kungiyoyin mata da iyayen sun yi taro suna kira a sako daliban. Wasu iyayen ma sun kuduri aniyar suyi zanga-zanga a Cibok domin nuna bacin ransu akan abunda suka kira rashin kulawa da lamarinsu daga hukumomi da jami'ai.

Gwamnatin Jihar Borno tayi alkawarin bada tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai kai ga ceto yaran mata.

A baya-bayannan ma, Gwamnan daya daga cikin jihohin dake da dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun gwamnati a rincabewar lamuran tsaro a arewarin Najeriya, zargin da gwamnati ta musanta, kuma wasu shuwagabanni a Najeriya da dama suka yi ta sukan gwamna Nyakon. Har yanzu tsohon hafsin rundunar sojin ruwa bai janye kalamunsa ba, wanda a ciki harda tattara shaidu na kaiwa kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague, domin tuhumar Shugaba Jonathan da kisan kare dangi.

Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda ‘yan bindigar nan da aka fi sani da Boko Haram suke da karfi, wadanda suka fara tayar da kayar baya tun shekara ta 2009. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya tace zata shawo kan matsalar, amma kashe-kashen mutane da kone-kone bai tsaya ba.

A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG