Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 06:14

  Labarai / Afirka

  An Fara kirgen kuri'u a Saliyo A zaben Kasa Da Akayi Ranar Asabar.

  wata mace take jefa kuri'a a zaben Saliyo da aka yi ranar Asabar.wata mace take jefa kuri'a a zaben Saliyo da aka yi ranar Asabar.
  x
  wata mace take jefa kuri'a a zaben Saliyo da aka yi ranar Asabar.
  wata mace take jefa kuri'a a zaben Saliyo da aka yi ranar Asabar.

  An fara kidaya a kuri’u a Saliyo, bayanda al’umar kasar a jiya Asabar, suka jefa kuri’a, domin zaben sabon shugaban kasa, da wakilan majalisar dokokin kasar.
  Magoya bayan jam'iya dake mulkin kasar Saliyo APC, a wani gangami da shugaba Koroma ya halarta a birnin Freetown.Magoya bayan jam'iya dake mulkin kasar Saliyo APC, a wani gangami da shugaba Koroma ya halarta a birnin Freetown.
  x
  Magoya bayan jam'iya dake mulkin kasar Saliyo APC, a wani gangami da shugaba Koroma ya halarta a birnin Freetown.
  Magoya bayan jam'iya dake mulkin kasar Saliyo APC, a wani gangami da shugaba Koroma ya halarta a birnin Freetown.

  Wannan ne karo na uku da Saliyo take gudanar da zabe tun bayan kawo karshen yakin basasa a kasar a 2002. Rahotanni sun  ce mutane  sun dunguma zuwa rumfunan zabe tun da sanyin safiyar jiya Asabar, domin su kada kuri’ar su.

  Shugaban tawagar masu aikin sa ido kan zaben na Tarayyar Turai Richard Howitt, ya gayawa manema labarai cewa a safiyar jiyan an gunadar zaben cikin tsanaki, kuma jama’a sun fito sosai.

  Hukumar zaben kasar tana da kwanaki 10 daga ranar da aka yi zabe ta bayyana sakamako, idan babu daya daga cikin ‘yan takara tara da  suke neman shugabancin kasar da  ya sami kashi 55 cikin dari, an ayyana ranar 8 ga watan Disemba, domin a  gudanar da zaben fidda gwani.

  Shugaban kasar wadda yake kan mulki yanzu, Ernest Bai Koroma, wanda ake yabawa da ayyukan gina kasa, yana fuskantar ‘yan hamayya takwas ciki har da babban abokin takararsa Julius Ma’ada Bio, wanda shine shugaban mulkin sojan kasar na wani  dan gajeren lokaci a 1996, kamin ya mika mulki ga gwamnatinn farar hula wacce ita ma bata juma ba.
  Magoya bayan daya daga jam'iyun hamayya suke maci a kan titin babban birnin kasar.Magoya bayan daya daga jam'iyun hamayya suke maci a kan titin babban birnin kasar.
  x
  Magoya bayan daya daga jam'iyun hamayya suke maci a kan titin babban birnin kasar.
  Magoya bayan daya daga jam'iyun hamayya suke maci a kan titin babban birnin kasar.

  Kakakin hukumar zaben kasar Albert Massaquoi, ya gayawa MA cewa hukumar ta dauki matakai domin tabbatarda sahihancin zaben da  suka hada da horasda ma’aikata. Kuma yace hukumar zata gaggauta bayyana sakamakon zaben fiye da abunda ya faru a baya.

  Shugaba Koroma ya sami nasarar zama  shugaban kasa, bayan lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a 2007. Ahlin yanzu jam’iyyarsa ta APC ce take rike da kujeru mafiya rinjaye a majalisar dokokin kasar.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye