Asabar, Maris 28, 2015 Karfe 10:18

Afirka

An Goce Da Wani Sabon Fada A Mali : Sojojin Cadi 13 Dana Mayakan Sakai 65 Sun Mutu.

Sojojin Mali suke bude wuta kan maboyar mayakan sakai a Gao.Sojojin Mali suke bude wuta kan maboyar mayakan sakai a Gao.
x
Sojojin Mali suke bude wuta kan maboyar mayakan sakai a Gao.
Sojojin Mali suke bude wuta kan maboyar mayakan sakai a Gao.
Aliyu Imam
A Mali an goce da sabbin fadace-fadace a sassa biyu na arewacin kasar inda  sojojin Faransa da wasu kasashen Afirka suke dafawa dakarun Mali, a fafatawar da suke yi na tusa keyar mayakan sakai ‘yan gani-gashenin Islama.

Wakilin Muriyar Amurka na Sashen Faransa yace kungiyar ‘yan tawayen abzinawa mai lakanin MNLA tana fafatawa yau Asabar da wata kungiyar mayakan sakai da ba'a bayyana sunanta ba, kusa da wani gari da ake kira Tessalit.

A jiya jumma’a wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a harabar kungiyar ‘yan tawayen abzinawa kusa da garin Tessalit, ya kashe mutane biyar, ciki har da mutane biyu da ake zargin sune ‘yan harin kunar bakin waken.

Ahalinda ake ciki kuma, shugaban Faransa, Francois Hollande yace dakarun kasarsa da na Cadi suna gwabza fada da mayakan sakai a yankin Ifoghas mai tsaunuka kusa da kan iyakar kasar da Aljeriya. Mr. Hollande ya fadawa manema labarai yau Asabar cewa dakarun sun hakikance cewa gungun hadakar ‘yan ta’adda suna neman mafaka cikin tsaunukan.

A jiyan rundunar sojojin Cadi daga cadin ta fada cewa an kashe mata sojoji 13, a kuma kashe ‘yan gani kashenin Islama su 65 a wani kazamain fada da aka gwabza a yankin Ifoghas din.
Cadi tana da sojoji dubu daya da dari shida a Mali.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti