Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Ministan Tsaron Korea Ta Arewa


Ministan Tsaro Korea Ta Kudu, Hyon Yon Chol.
Ministan Tsaro Korea Ta Kudu, Hyon Yon Chol.

Hukumar tattara bayanan sirrin kasar Korea ta Kudu, tace shugaban kasar Korae ta Arewa, Kim-Jong Un, yasa an harbe Ministan tsaron kasar saboda bacci ya kwashe shi yayin da ake wani taron sojoji.

An dai kashe sojan saman mai mukamin Vice Marshall Hyon Yon Chol ne ta hanyar bindigewa. Daruruwan jami’an gwamnatin ne suka shaida hukuncin kisan, wanda aka aiwatar a ranar 30 ga watan Aprilu, kamar yadda mataimakin darektan hukumar tattara bayanan sirrin Han Ki-Beom ya bayyanawa kwamitin majalisar a birnin Seoul.

Kamfanin Dillancin labaran Korea ta Kudu na Yonhap, yace Mr. Kim, ya amince cewa baccin da Ministan tsaron ya yi, alama ce da ke nuna rashin biyayya da girmamawa. Ko da yake akwai rahotanni da suka nuna cewa Ministan ya sha kalubalantar Shugaba Kim kan wasu batutuwa da dama.

A Korea ta Arewa, Ministan Tsaro, shi ke da alhakin shirya huldar musanya tsakanin kasashe. Sannan kwamitin Tsaro da na dakarun Kasa su ke da alhakin yin tsare-tsaren al’amuran kasar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG