Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kada Kuri’ar Tsige Shugaban Madagascar


Madagascar Pothole Politics
Madagascar Pothole Politics

Yan Majalisar dokokin kasar Madagascar, sun kada kuri’ar amincewa da tsige shugaba kasar, a wani mataki da wasu ke ganin ka iya tsunduma kasar cikin sabon rikici.

Wannan yunkuri na tsige shugaba Hery Rajao-na-rimam-pia-nina ya samu goyon bayan ‘yan majalisu 121 daga cikin ‘yan majalisu 125 da suka kada kuri’unsu a yau laraba.

Yanzu ya rage ne kotun kundin tsarin mulkin kasar ta duba matsayar wannan kuri’a da aka kada, kafin a dauki mataki na gaba.

Shugaba Rajao-na-rimam-pia-nina, ya karbi mulkin kasar ne a watan Janairun bara, bayan komawa karkshin turbar dimokradiyya da kasar ta yi a shekarar 2006.

An sa ran, mulkin shugaban zai kawo karshen tarzomar siyasar da ta addabi kasar bayan da aka hambarar da gwamnatin Marc Ravalomanana a shekarar 2009.

Sai dai masu adawa da mulkin shugaban kasar na yanzu, sun yi ikrarin cewa gwamnatin ta gaza, kuma lokaci ya yi da za a kawar da ita.

A baya kasar Amurka ta nuna goyon bayan ta ga shugaba Ery, a shekarar da ta gabata ne kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta cire dukkanin shingayen baiwa kasar taimako, saboda nasarar zaben da aka yi, wanda ya samar da sabuwar gwamnati.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG