Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe akalla mutane goma a Niger, a sakamakon zanga zanga.

Shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou
Shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou

Shugaban jamhuriyar Niger Mahammadou Issoufou yace an kashe akalla mutane goma a mumunar zanga zangar kwanaki biyu da aka yi domin nuna rashin amincewa ga zanen da Mujjalar Charlie Hebdo ta kasar Faransa tayi na batunci ga Anabbi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Shugaba Muhammadou Issoufou yace jiya Asabar an kashe mutane biyar lokacinda aka bankawa coci coci wuta a mumunar arangamar da aka yi a Niamey baban birnin kasar. Sa'anan kuma a ranar Juma'a aka kashe mutane biyar a birnin Zinder dake kudancin kasar.
Mai magana da yawun jam'iyar PNDS Tarayya, Sani Iro yace gwamnatin Niger ta yanke shawarar daya kamata na haramta rarraba Mujallar Charlie Hebdo. Yace gwamnatin Niger ta dauki wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
To amma kuma masu caccakar wannan mataki, sunce daukan matakin ya keta ka'idar yancin fadin albarkacin baki, yancin dake cikin tsarin mulkin kasar.
Mumunar zanga zangar da aka yi a jamhuriyar Niger, wadda Faransa ta taba yiwa mulkin mallaka ya hada harda harin da aka kaiwa cibiyar al'adu ta Faransa. Jiya Asabar ofishin jakadancin Faransa a Nigeria ya yiwa Faransawa kashedin cewa su guji fita a titunan kasar.
Haka kuma an yi mumunar zanga zangar a birnin Karachi na kasar Pakistan inda daruruwan masu zanga zanga suka yi arangama da 'yan sanda. Wasu biranen kasar da aka yi zanga zanga su hada harda Islamabad baban birnin kasar da birnin Lahore.

XS
SM
MD
LG