Lahadi, Nuwamba 29, 2015 Karfe 22:12

Labarai / Sauran Duniya

An Harbe Aka Kashe 'Yan Zanga-Zanga Uku A Masar.

Magoya bayan shugaba Morsi, da masu adawa suka baiwa hamata iska a harabar fadar shugaban kasa a Alkahira, ranar laraba.Magoya bayan shugaba Morsi, da masu adawa suka baiwa hamata iska a harabar fadar shugaban kasa a Alkahira, ranar laraba.
x
Magoya bayan shugaba Morsi, da masu adawa suka baiwa hamata iska a harabar fadar shugaban kasa a Alkahira, ranar laraba.
Magoya bayan shugaba Morsi, da masu adawa suka baiwa hamata iska a harabar fadar shugaban kasa a Alkahira, ranar laraba.
An harbe aka kashe akalla masu  zanga- zanga uku a Alkahira, babban birnin kasar Masar jiya laraba, a wasu rangamomi tsakanin magoya da masu adawa da shugaba Mohammed Morsi.An cigaba da  tarzomar har zuwa safiyar yau Alhamis. Akwai rahotanni da suke cewa fiye da mutane 300 kuma sun jikkata.

Rahotanni daga inda ake rikicin daga wakiliyar Muriyar Amurka, ta ce sabon tarzomar ta barkene lokacinda magoya bayan Mr. Morsi masu ra’ayin islama, suka kai hari kan masu zanga-zangar nuna adawa kan abunda  suka kira babakere kan madafun iko da shugaba Morsi yayi.

Arangamar da aka yi a sansanin fadar shugaban kasar, itace irinta ta farko da ‘yan hamayya a kasar wacce ta rabu gida biyu kan ra’ayin siyasa suka baiwa hamata iska, tun zanga zangar bara wacce ta tilastawa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak yin murabus.

A gefe daya kuma, wasu hadiman shugaba Morsi uku sun bada sanarwar yin murabus, domin bayyana rashin amincewarsu kan dokar shugaban kasar wacce ta bashi dumbin iko. Biyar daga cikin masu baiwa shugaban kasar shawara 17, sun yi  murabus daga 22 ga watan jiya.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye