Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 13, a sakamakon kai hari a Afghanistan


Sojojin Afghanistan ke gadi a wani wuri da aka kai harin bam
Sojojin Afghanistan ke gadi a wani wuri da aka kai harin bam

Wani hari da aka kai Kabul baban birnin kasar Afghanistan ya kashe mutane goma sha biyu, ciki harda wasu 'yan kwangila wadanda suke yiwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO aiki a kasar

A Kabul baban birnin kasar Afghanistan, wani harin bam da aka asibiti jiya Asabar ya kashe mutane goma sha biyu ciki harda Amerikawa guda uku yan kwangila wadanda suke yiwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO aiki a kasar.
Mutane da dama sunji rauni a tashin bam din daya ratsa har wata unguwa ya lalata ko kuma yayi kaca kaca da motoci da dama.


Kungiyar NATO bata baiyana sunayen yan kwangilan da aka kashe ba, amma tace nan take daya daga cikinsu ya mutu, saura biyun kuma sun mutu ne a lokacinda ake yi musu jinya.


Shedun gani da ido sunce harin ya auna kwamban sojojin kasashen waje wadanda suke wucewa a birnin kabul a yayinda suke wuce asibiti. Nan da nan ofishin jakadancin Amirka dake kusa ya busa jiniyansa yana yiwa mutane kashedin cewa su boye.


Nan da nan kuma, babu kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin, a hari na baya bayan nan cikin munanan hare hare da aka kai a wannan wata da suka kashe akalla mutane hamsin da raunana daruruwan mutane a birnin Kabul.


Mayakan Taliban sunce sune suka kaddamar da yawancin hare haren. Kungiyar Taliban ta kara kaimin hare haren da take kaiwa bayan da sojojin Amirka dana kungiyar NATO suka kawo karshen rawar da suke takawa wajen kokarin murkushe kungiyar a karshen shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.


Kodayake sojojin Amirka dana kungiyar NATO sun fice daga Afghanistan, har yanzu akwai kimamin sojoji dubu goma sha uku a kasar wadanda suke horar da sojojin Afghanistan dabarun dakile aiyuka ta'adanci.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG