Talata, Mayu 03, 2016 Karfe 19:12

  Labarai / Kiwon Lafiya

  An Kusa Samun Maganin Zazzabin Cizon Sauro Mai Karfi

  Wata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauroWata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro
  x
  Wata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro
  Wata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro
  Masu ilimin kimiyya sun samu cin gaba a neman maganin da zai iya kashe zazzabin cizon sauro da za a sha sau daya kawai ba kari, wanda banda jinyar wanda ya kamu da cutar, zai kuma zama rigakafi da garkuwa ga wanda ya sha maganin.

  Ana kyautata zaton za a fara gwajin kaifin maganin ne a karshen wannan shekarar ta dubu biyu da goma sha uku wanda ake gani zai taimaka wajen ceton rayukan miliyoyin mutane a kasashen nahiyar Afrika.

  Wannan ne maganin farko da za a sarrafa daga binciken da aka faro a Afrika da ‘yan nahiyar Afrika da kansu suka gudanar.

  Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana zazzabin cizon sauro a matsayin cutar da tafi kowacce kisa, da take kashe kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyu kowacce shekara da suka hada da kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba, da kuma mata masu ciki.

  Najeriya tafi kowacce kasa a duniya fama da zazzabi cizon sauro inda kimanin mutane dubu dari uku suke mutuwa da dalilin kamuwa da cutar kowacce shekara.

  Watakila Za A So…

  Sauti Ranar Bukin Yancin Yan Jarida Ta Duniya

  Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 3 ga watan Mayu domin bukin ranar yancin yan jaridu, taken bukin bana dai shine samar da yanci na yada labarai a matsayin daya daga cikin yacin bil Adama da kuma kare yan jaridu wajen gudanar da ayyukansu ba tare da sa musu tukunkumi ba, da kuma tabbatar da lafiyarsu. Karin Bayani

  Sauti Kungiyoyin Kwadago Kan Neman Gwamnatin Najeriya Ta Kara Mafi Karancin Albashi

  Neman karin mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadagon Najeriya sukayi a ranar ma’aikata ta bana da alamu bai samu kwakkwarar amsa daga gwamnatin da ke famar karbar kasafin kudi, daga Majalisa da nufin fara wasu ayyuka da masu zabe zasu fara shaidawa. Karin Bayani

  Sauti Dokar Yadda Za’a Gudanar Da Wa’azi A jihar Kaduna Na Gaban Majalisar Jihar

  Har ya zuwa yanzu dai dokar da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufa’i ya kaiwa majalisar dokokin jihar game da yadda Mallaman addinin Krista da Musulmi zasu gudanar da wa’azi tana gaban Majalisar. Karin Bayani

  Shugaba Obama yace tun ranar da ya kama mulki ya kuduri aniyar kashe Osama Bin Laden

  Matakin farautar kashe shugaban kungiyar ta’addar Al-Qaida Osama Bin Laden shine a sahun gaba na abubuwan dana kuduri aniya yi tun lokacin da na zama Shugaban kasar Amurka. Karin Bayani

  Trump ne ke kan gaba a jihar Indiana a zaben fidda gwani na Republican

  Dan takar neman jam’iyyar Republican ta tsayar da shi takarar shugabancin Amurka na sahun gaba Donald Trump, yana haramar fuskantar daya daga zabukan fidda gwani mai wahala, wato zaben na jihar Indiana. Karin Bayani

  'Yan Shi'a sun janye zanga zangarsu a Bagdaza

  A jiya Litinin kura ta lafa a birnin Bagdaza, biyo bayan tarin masu zanga-zangar da suka mamaye wata unguwar da ke da ofisoshin kasashen duniya tun ranar Asabar. Karin Bayani

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye