Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: An Tarwatsa Mutanen Wata Mazabar Taraba


Akwatunan Zabe
Akwatunan Zabe

Ana ci gaba da kada kuri'a a jihar Taraba a zaben raba gardamar da ake yi a yanzu haka. Sai dai wasu bata gari sun tarwatsa wasu jama'ar da ke kokarin yin zabe a wata mazaba.

An bude rumfunan zabe a daidai lokacin da aka ce za a bude a Jihar Taraba. In dai ba a manta ba an yi zaben gwamnoni a Najeriya ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2015. To amma a wasu jihohin an sami tangardar da ta sa dole aka soke zaben da niyyar sake wa.

Jihohin sun hada dairin su Taraba da Imo. A yau din ake sake zabukan kamar yadda aka sanar daga ofishin hukumar zabe ta INEC. An rarraba kayan a mazabu dari da sittin da biyar da ke Taraba din tare da ma’aikata. Haka kuma an sami isar jami’an tsaro da ke sintirin kare lafiyar al’umma.

Amma a Mazabar Malam Bello an sami wasu matasa da suka far wa jama’ar da suka halarci wajen don yin zabe. Jama’a sun tarwatse don tsira da lafiyarsu. Wasu shedu a wajen sun fadawa wakilin Muryar Amurka cewa, sanadin rikicin shine an sami ‘yan wasu mazabun ne da suka je wajen don yin zabe.

Da aka nemi a hana su yi ne kuma sai hatsaniyar ta kaure inda jama’a suka shiga yin takansu don kar a musu aika-aika. To amma dai a yanzu haka jama’a na ta kada kuri’arsu a kananan hukumomi goma sha shida.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG