Alhamis, Mayu 05, 2016 Karfe 19:03

  Labarai / Afirka

  An Umarci 'yan Tawayen M23 Su Fice Daga Goma

  wani soja yana kallon dubban mutanen da suka halarci gangamin 'yan tawayen M23 a Goma.
  wani soja yana kallon dubban mutanen da suka halarci gangamin 'yan tawayen M23 a Goma.
  Shugabannin kasashen Afirka ta tsakiya uku sun ce tilas ne ‘yan tawayen da suka kwace Goma su janye ba tare da bata lokaci ba.

  Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila, da takwaransa na kasar Rwanda Paul kagame da kuma na Uganda Yoweri Museveni sun fitar da sanarwar hadin guiwa jiya Laraba bayan ganawarsu a Kampala babban birnin kasar Uganda. 

  Shugabannin sun ce tilas ne kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta daina kai hari ta kuma janye daga Goma. Sun kuma ce gwamnatin Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango tayi alkawarin gudanar da bincike domin tantance masababin tashin hankalin.

  Shugabannin Uganda da na Rwanda sun bayyana goyon bayan gwamnatin Damokaradiyar Kwango wadda ‘yan tawayen suka lashin takobin hambararwa.

  Damokardiyar Jamhuriyar Kwango tana zargin Rwanda da kuma Uganda da goyon bayan kungiyar M23. Zargin da kasashen biyu suka musanta.

  ‘Yan tawayen M23 sun gudanar da gangami a babban filin wasan Goma jiya Laraba, kwana daya bayan sun kwace garin, wanda shelkatar lardi ne dake kan iyaka da Rwanda. Kakakin kungiyar Viianny Kazarama yace ‘yan tawayen suna niyar ci gaba.

  Yace “Shugaba Kabila ya kawo jiragen yaki da manyan bindigogi, amma bai iya samun nasara bisanmu ba. Wannan manuniya ce cewa, muna cikin shirin Allah; Allah ne ya aiko mu kuma wannan ba zata tsaya a nan ba.”
  Daruruwan ‘yan sandan kasar Kwango da kuma sojoji sun mika makamansu a wajen gangamin.

  Kazarama yace burin ‘yan wayen na gaba shine su kwace Bukavu dake tazarar kilomita 100 da kudancin kasar. Yace tuni kungiyar ta kwace ikon Sake, wani gari dake kudancin Goma, kungiyar kuma tana niyar isa Kinshasa babban birnin kasar, dake tazarar kilomita dubu daya da dari biyar zuwa yammaci.

  Jiya Laraba har wa yau, babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango Roger Meece yace ‘yan tawayen suna kashe shugabannin al’umma a Goma wadanda suke bijire masu. Kawo yanzu kungiyar ‘yan tawayen bata maida martani dangane da zargin keta hakin bil’adama ba.

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye