Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Ranar Kwastan ta Duniya a Abuja


Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar. (File Photo)
Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar. (File Photo)

An gudanar da bikin ranar kwastan ta duniya a Abujan Najeriya.

Hukumar kwastan ta Najeriya a karkashin shugabancin Abdullahi Inde ta shirya bitoci da lacca lacca.

A cikin bitocin da manyan jami'an kwastan din suka gabatar sun nuna irin cigaban da suka samu wanda ya shiga tarihi na tara dubban dubatan miliyoyin nera wa kasar.

Shugaban hukumar Abdullahi Dikko Inde yace anfanin da aka yi na sauye-sauye da canje canje akan anfani da naura mai kwakwalwa wurin aikin hukumar ya inganta ayyuka da nasarorin da suka samu a yanzu.

Shugaban yace shekara guda ke nan da suka kwace aikinsu da aka baiwa 'yan kasashen waje. Yanzu kudin shiga ya karu ana kuma samun cigaba. 'Yan Najeriya sun yaba kuma an samu fahimta da mutane da suka ba hukumar hadin kai. Duk wanda da suke aikin da ya shafi kwastan sun basu hadin kai.

Da 'yan kwangilar da aka kawo daga kasashen waje ana biyansu nera biliyan 57 da miliyan bakwai a shekara ko sun yi aikin ko basu yi ba kuma ba tare da tuntubar hukumar ba. To yanzu gwamnati bata asarar wadannan kudaden.

Ga rahoton Umar Faruk.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG