Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Rev Musa Tsakani


Rev. Musa Tsakani
Rev. Musa Tsakani

An yi jana’izar Rev. Musa Tsakani mai bisharar da ake kyautata zaton shine yafi kowanne limamin kirista a arewacin Najeriya tsufa da kuma dadewa a aikin bishara.

An yi jana’izar Rev. Musa Tsakani mai bisharar da ake kyautata zaton shine yafi kowanne limamin kirista a arewacin Najeriya tsufa da kuma dadewa a aikin bishara.

An haifi Rev Musa Tsakani a ranar biyar ga watan biyu na shekarar alib dubu da dari tara daidai a Dot, karamar hukumar Dass ta jihar Bauchi. Ya tuba zuwa addinin Kirista a shekara ta dubu da dari tara da ishirin da shida. Ya kuma fara makarantar Littafi Mai Tsarki a shekara ta dubu daya da dari tara da ishirin da tara zuwa da talatin. Rev. Musa Tsakani yayi ayyukan Bishara a jihohi da dama a Najeriya. Ya yi ritaya a cikin shekara ta dubu da dari tara da tamanin da takwas.

Ya rasu ya bar matarsa alheri da ‘ya’ya takwas da jikoki talatin da uku da tattaba kunne ishirin da takwas. Jama’a daga ciki da wajen Najeriya da suka halarci jana’izarsa sun bayyana marigayin a matsayin mai tsoron Allah da hada kan al’umma wanda yake rungumar kowa ya kuma kasance uba ga kowa ba tare da kula da banbancin kabila ko addini ba.

A cikin jawabinsa, sarkin Dass mai martaba Usman Bilyaminu Usman ya bayyana marigayin a matsayin uba mai hangen nesa wanda ya bada gudummuwa ga ci gaban kasancewar masarautar tsintsiya madaurinki daya.

Wakiliyarmu Zainab Babaji ta halarci jana’izar ta kuma hada wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG