Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi 'Yansandan Mexico da Hannu a Bacewar Wasu Dalibai 43


Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto
Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto

Shugaban kasar Mexico yace za'a hukunta duk wadanda aka samesu da hannu a bacewar dalibaai 43 biyo bayan gano wasu gawar waki 7 a wani rami

Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto yace, “babu wanda za’a kare” kan bacewar dalibai 43 masu zanga zanga, a zargi da ya shafi wasu jami’an ‘Yansandan kasar.

Shugaba Enrique yayi taro da manema labarai jiya Litinin, domin yayi magana kan wannan batu, kwanaki biyu bayan da aka gano wani babban rami da aka binne mutane a jihar da ake kira Guerrero. Babban lauyan gwamnati yace akwai dangantakar bacewar daliban da kuma abunda aka gano a ramin, duk da haka masu bincike suna dakon sakamakon tantancewar kimiyya da ake kira DNA.

Shugaba Nieto yace bacewar daliban “abun bakin ciki ne, da hukuma ba zata lamunta da haka ba. Yace kasar Mexico da iyalan daliban suna da damar su nemi sanin hakikanin abunda ya faru, kuma su bukaci ganin an yi adalci, kuma duk wadanda aka samu suna da hannu cikin wannan aika-aikar su fuskanci hukunci, domin babu shafaffu da mai.

Wani mai gabatar da kara yace wasu ‘yan kisan kai daga wasu kungiyoyin banga biyu, sun tabbatar cewa sun taimakawa ‘Yansanda suka kashe 17 daga cikin daliban wadanda suka bace kwanaki 10 da suka wuce.

XS
SM
MD
LG