Talata, Fabrairu 09, 2016 Karfe 12:41

  Labarai / Kiwon Lafiya

  Ana Iya Shawo Kan Zazzabin Cizon Sauro -Hukumar Lafiya Ta Duniya

  Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, ana iya shawo kan zazzabin cizon sauro. Majalisar Dinkin Duniya tace zuba jari a kan yaki da zazzabin cizon sauro zai taimaka a yunkurin kula da lafiyar al’umma.

  Ana bama dan yaro maganin cutar cizon sauro.
  Ana bama dan yaro maganin cutar cizon sauro.
  Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, ana iya shawo kan zazzabin cizon sauro. Majalisar Dinkin Duniya tace zuba jari a kan yaki da zazzabin cizon sauro zai taimaka a yunkurin kula da lafiyar al’umma.

  Zazzabin cizon sauro yana daya daga cikin cututakan da suka fi kashe mutane a duniya. Hukumar Lafiya tayi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan dubu dari uku da talatin  suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar a shekara.

  Hukumar lafiya ta bayyana cewa, ko da yake ana iya shawo kan zazzabin cizon sauro, yana ci gaba da kama sama da mutane miliyan dari biyu yayinda yake kuma kashe kimanin mutane dubu dari shida da sittin kowacce shekara.

  Duk da haka hukumar ta bayyana cewa, ana iya cimma burin muradun karni na shawo kan cutar kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar. Hukumar lafiyar tace kawo yanzu kasashe hamsin sun yi nisa a yunkurin cimma burin shawo kan cutar da kimanin kashi 75% a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

  Hukumar Lafiya ta bayyana cewa, shirin yaki da zazzabin cizon saura na kasa da kasa ya taimaka wajen ceton rayukan mutane miliyan daya da dubu dari da kuma jinyar kimanin mutane miliyan dari biyu da saba’in da hudu tsakanin shekara ta dubu biyu da daya zuwa dubu biyu da goma. Bisa ga cewar hukumar  ana samun kashi 80% na zazzabin cizon sauro ne a kasashen da cutar tayi muni, kashi 40% daga ciki kuma daga kasashe uku da aka fi fama da zazzabin cizon sauro da suka hada da Najeriya, da Congo da kuma India.

  Babbar kalubalar da ake fuskanta a halin yanzu a yaki da cutar shine, kin jin magani da kwayar cutar zazzabin cizon sauro take yi.

  Watakila Za A So…

  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5! Yau da Gobe ya hada komai, daga filin dafe-dafen gargajiya, zuwa zauren matasa inda suke bayyana ra’ayoyin su daban-daban akan wasanni, da siyasa, da mu’amala ta samari da ‘yan mata, da fasaha, da filin kiwon lafiyar matasa.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye